Wasu ‘yan bindiga sun sace ɗalibai bakwai na makarantar gwamnati da ke Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar Zamfara bayan sun kai hari a daren Alhamis. Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kutsa yankin ne da makamai tare da yin awon gaba da ɗaliban zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Majiyoyi sun ce lamarin ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin da iyalan daliban, yayin da jami’an tsaro suka fara ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace. Haka zalika, an ce an sanar da hukumomin tsaro nan take bayan faruwar harin.
Bayan harin, jami’an tsaro sun fara sintiri da bincike a yankunan da ake zargin maharan suka bi domin gano maɓoyarsu da kuma kuɓutar da ɗaliban. Lamarin na ƙara nuna yadda matsalar satar mutane ke ci gaba da addabar wasu sassan Jihar Zamfara.
Harin na zuwa ne yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin daƙile ayyukan ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma. Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa kan kuɓutar da daliban ko kama waɗanda suka kai harin.





