Abubuwan Da Ya kamata Ka Sani Kan Garan Bawul Da FG Zata Yiwa NYSC

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da yin garambawul kan shirin bautar ƙasa na NYSC, karo na farko tun bayan kafuwarsa shekaru 53 da suka gabata, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

Sabbin sauye-sauyen na da nufin mayar da NYSC cibiyar da za ta fi mayar da hankali kan koyar da ƙwarewar sana’o’i, haɓaka aiki da bunƙasa matasa domin tallafa wa manufofin tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya.

Daga cikin muhimman sauye-sauyen akwai:

Maye gurbin shugaban NYSC na soja da shugaba na farar hula.

Sojoji za su ci gaba da ba da kariya ga masu yi wa ƙasa hidima.

Za a yi amfani da fasaha wajen tsarin kiran masu yi wa ƙasa hidima (call-up).

Za a inganta tsarin tura matasa zuwa jihohi ta hanyar la’akari da tsaro.

Za a sake fasalin horon sansanin na makonni shida, tare da ƙarfafa koyar da shugabanci, kasuwanci da ƙwarewar zamani.

Za a daidaita wuraren aikin yi wa ƙasa hidima da fannin karatun kowane matashi.

Za a inganta sansanonin NYSC ta hanyar sabon tsarin tantance inganci.

Za a maye gurbin bikin Passing Out Parade da sabon bikin kammala hidima.

Haka kuma, za a ƙaddamar da sabbin kayan sanya na NYSC domin su nuna ƙwarewa da kishin ƙasa.

Ministan Matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa waɗannan sauye-sauye za su taimaka wajen gina matasa masu ƙwarewa tare da dacewa da burin Shugaba Bola Tinubu na bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.

Har ila yau, ya ce za a gyara dokar NYSC domin ba da cikakken goyon bayan doka ga aiwatar da waɗannan sauye-sauye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *