Tauraron ɗan wasan baya na ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, na ci gaba da kafa tarihi a duniyar ƙwallon ƙafa bayan tara manyan kofuna a matakin ƙungiyoyi da ƙasa duk da cewa yana da shekara 27 kacal. Nasarorin da ya samu sun sanya shi cikin fitattun ‘yan wasan Afirka mafiya cin nasara a zamanin nan.
Hakimi ya lashe kofin Ligue 1 sau biyar a Faransa, UEFA Champions League sau uku, Coupe de France sau biyu, UEFA Super Cup sau biyu, tare da lashe La Liga a Sifaniya da Serie A a Italiya. Bugu da ƙari, ya kuma lashe FIFA Club World Cup, Spanish Super Cup, German Super Cup da FIFA Intercontinental Cup.
- Dangote Zai Samar Da Ayyukan Yi Ga Mutane 90,000 A Legas
- Bani Da Tabbacin Ci Gaba Da Zaman A Real Madrid
- Tinubu Ya Amince Da Ƙarawa Yan Fansho Kuɗi
- Abubuwa 30 Da Suke Kawo Mutuwar Aure Tsakanin Ma’aurata
- Illoli 20 Na Zina Masu Haɗari
A matakin ƙasa, ɗan wasan ya taimaka wa Morocco wajen lashe kofin Afirka, lamarin da ya ƙara wa tarihin nasarorinsa armashi. Haka kuma, ya taka leda a wasu manyan ƙungiyoyin Turai da suka haɗa da Real Madrid, Borussia Dortmund, Inter Milan da Paris Saint-Germain.

A shekara 27 kacal, Hakimi ya riga ya lashe kusan dukkan manyan kofunan da ɗan wasa zai yi mafarkin samu a Turai da Afirka. Wannan nasara ta sa mutane da dama ke kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin mafiya ƙwarewa da nasara a tarihin ‘yan wasan baya na nahiyar Afirka.





