Annobar Kwalara Ta Hallaka Mutane 37, Ta Kama Fiye Da Mutane 3,000 A Borno

Gwamnatin Jihar Borno ta bayyana cewa annobar kwalara ta yi ajalin mutane 37 tare da kama fiye da mutum 3,000 a cikin watan Mayu kaɗai a ƙananan hukumomi bakwai na jihar. Rahotanni sun nuna cewa annobar na ci gaba da yaɗuwa yayin da ake shiga lokacin damina.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya ta Borno (BOSCHMA), Dakta Saleh Abba-Kaza, ya ce an fara samun rahoton bullar cutar ne a ranar 1 ga Mayu, kafin a tabbatar da ita a ranar 4 ga watan. Ya ƙara da cewa fiye da sabbin mutum 100 sun kamu da cutar cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yayin da Maiduguri ke kan gaba da fiye da mutum 2,000 da suka kamu, sai Jere da sama da mutum 1,000.

A cewarsa, annobar ta bazu zuwa unguwanni 36 da fiye da al’ummomi 138 a ƙananan hukumomin Maiduguri, Jere, Mafa, Konduga, Monguno, Ngala da Magumeri. Ya danganta yaɗuwar cutar da matsalolin tsaftar muhalli, gurɓacewar hanyoyin ruwa da kuma ci gaba da yin bahaya a fili a wasu yankuna.

Dakta Abba-Kaza ya buƙaci mazauna jihar su kula da tsaftar muhalli, su riƙa amfani da ruwan da aka tsarkake, su wanke hannu akai-akai, sannan su garzaya asibiti idan sun fara fama da amai ko gudawa.

Ya kuma yabawa Ma’aikatar Lafiya ta jihar da abokan hulɗarta da suka haɗa da Hukumar Lafiya ta Duniya, UNICEF da Médecins Sans Frontières kan matakan da suke ɗauka domin dakile annobar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *