Barazanar Da Ke Tattare Da Haihuwa A Gida A Arewa Maso Yamma Ya Zama Babban Kalubale

Gwamnatocin jihohi na Arewa maso Yamma dole ne su zuba kudi sosai a cikin Tsarin Lafiya na Mazabu (Ward Health System), su tabbatar da cewa asibitocin karkara na PHC suna da saukin zuwa, suna da kwararrun ungozomomi mata, da kuma wadatar kayan haihuwa kyauta ko masu arha. Haka kuma, dole ne a hada hannu da sarakunan gargajiya da na addini domin wayar da kai da sukar duk wasu al’adu da ke hana zuwa asibiti.