Dalilai 2 Da Ke Sa Mutane Shiga Ƙungiyoyin Ta’addanci – Ministan Tsaro

Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana cewa manyan abubuwa biyu ne ke jawo mutane shiga ƙungiyoyin ta’addanci.

A cewarsa, wasu na shiga ne saboda an yaudare su da cewa suna yaƙi ne domin addini ko kuma suna gudanar da abin da Allah ya umarta.

Ya kuma ce talauci na daga cikin manyan dalilan da ke sa wasu shiga irin waɗannan ƙungiyoyi, domin suna ganin hakan ne kaɗai hanyar samun kuɗi da rayuwa.

Ministan ya jaddada muhimmancin yaƙi da talauci da kuma wayar da kan jama’a a matsayin hanyoyin rage yawaitar ta’addanci a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *