Gwamnatin Kano Ta Waiwayi Fannin Ruwan Sha, Ta Bayar Da Kwangilar Naira Biliyan 21.29

The Kano State Government

Gwamnatin Jihar Kano ta sanya hannu kan kwantiragin da ya kai Naira biliyan 21.29 tare da kamfanonin gine-gine na ƙasar China guda biyu domin gyaran manyan cibiyoyin samar da ruwa a faɗin jihar. Aiyukan da za ayi za su haɗa da gyaran cibiyoyin tace ruwa na Tamburawa da Challawa domin inganta samar da tsaftataccen ruwan sha da farfaɗo da muhimman kayayyakin more rayuwa.

A cikin wata sanarwa da mukaddashin kwamishinan albarkatun ruwa, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa kamfanin CGC Nigeria Limited zai gudanar da gyaran cibiyar tace ruwa ta Tamburawa da tashar famfon ɗebo ruwa a kan Naira biliyan 9.9, yayin da CCECC Nigeria Limited zai gyara tashar famfon ruwa da cibiyar tace ruwa ta Challawa tare da maido da tankunan Goron Dutse a kan Naira biliyan 11.39.

Bugu da ƙari, Dakta Hashim ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan cewa kamfanonin za su kammala ayyukan cikin watanni takwas kamar yadda aka tsara. Ya ƙara da cewa gyaran zai ƙara yawan samar da ruwa da inganta rabonsa musamman a birnin Kano da yankunan da ke dogaro da waɗannan cibiyoyi.

A ƙarshe, ya ce aikin wani ɓangare ne na ƙudirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na magance matsalolin ruwa da samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’umma. Haka kuma, kamfanonin sun tabbatar da shirinsu na gudanar da aikin cikin lokaci tare da kiyaye inganci, yayin da ma’aikatar ta yi alƙawarin sanya ido sosai domin tabbatar da gaskiya da nasarar aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *