Bayanai na nuna cewa tattalin arzikin Najeriya yana samar da manyan lambobi na kudin shiga, amma idan aka yi nazari na tsanaki, za a ga cewa wasu jihohin ne ke yin babban aiki yayin da wasu ke dogara da su.
Bisa ga sabbin bayanai daga Kwamitin Raba Kudade na Tarayya (FAAC) da shafin TheCableIndex ya wallafa, Najeriya ta tara zunzurutun kudi har triliyan ₦3.78 a matsayin Harajin Kayayyaki da Ayyuka (VAT) a farkon rabin shekarar 2026 (daga watan Janairu zuwa Yuni).
To amma ga babban abin mamakin: kusan rabin wannan uban kudin gaba daya ya fito ne daga jiha guda daya kacal wato Jihar Lagos, wadda ta tara triliyan ₦1.81 (kimanin kashi 47.9%).
Ina Jihar Kano Take A Wannan Fafatawa?
A matsayinta na cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya, Jihar Kano ta sami nasarar tara biliyan ₦65.21, wanda hakan ya ba ta damar zama ta 7 a jerin jihohin da suka fi kowace jiha tara kudin VAT a fadin kasar. A zahiri, wannan kamar babbar nasara ce. Amma idan aka kwatanta wannan biliyan ₦65.2 da dimbin jama’ar da ke Kano da kuma manyan ayyukan ci gaba na biliyoyin nairori da gwamnati ta sa a gaba, sai a ga cewa akwai babban kalubale.
Jadawalin Jihohi 10 Da Suka Fi Tara VAT (H1 2026)
Kafin mu shiga cikin fashin baki kan Jihar Kano, ga yadda manyan jihohi 10 na farko suka fafata a cikin watanni shida na farkon shekarar nan:

Abu mai muhimmanci da ya kamata a sani: Idan aka dubi kasan teburin, jihohi kamar Abia (₦8.77bn) da Cross River (₦10.55bn) suna fafutukar ganin sun tsallake shingen ₦10 biliyan. Hasali ma, sauran jihohi 27 da suka rage idan aka hada kudadensu wuri guda, ba su kai ko kashi 15% na jimillar kudin VAT na daukacin kasar nan ba.
Matsalar Tattalin Arzikin Kano: Kasuwanni Masu Girma, Amma Karancin Haraji
Idan ka ratsa ta cikin lungu da sako na kasuwar Kantin Kwari, ko ka yi duba ga dumbin hada-hadar da ke gudaba a kasuwar Sabon Gari da sauran kasuwanni kamar Kasuwar Dawanau, Kasuwar Wayoyi, Kasuwar Magani, Kasuwar Kurmi da Sauransu, za ka ga yadda biliyoyin nairori ke musayar hannu a kullum. Babu shakka Kano ita ce cibiyar kasuwanci mafi girma a Arewa.
To, me ya sa kason da ta bayar na kudin VAT na kasa ya tsaya a iya kashi 1.7% kacal?
Babban dalilin shi ne mafi yawan harkokin kasuwancin Kano na fannin da ba a yi masa rajista ba ne (informal economy). Har yanzu hada-hadar tsabar kudi (cash) ita ce mafi girma, wanda hakan ke sa miliyoyin nairori na harajin sayayya ke sulalewa ba tare da sun shiga asusun gwamnati ba. Hukumar Tara Kudin Shiga ta Jihar Kano (KIRS) tana aiki sosai don canza tsarin zuwa na na’ura mai kwakwalwa (digitization), amma sauya tsarin tsohuwar kasuwa ta gargajiya yana daukar lokaci. Watakila saboda rashin tsauraran matakai ko gamsassun dabarun wayar da kai.
Me Yasa Wannan Ke Da Muhimmanci Yanzu?
A halin yanzu, Jihar Kano ta yi kasafin kudi mai ban mamaki na triliyan ₦1.47 na wannan shekarar, karon farko a tarihi. Domin gudanar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa, lafiya, da ginin azuzuwa da aka yi wa al’umma alkawari, gwamnatin jihar ta bayyana karara cewa tana bukatar kimanin ₦909.9 biliyan daga kudaden da FAAC ke rabawa.
- Kudin VAT da Aka Tara a Kano (H1): ₦65.21bn
- Kudin da Ake Kyautata Zaton Za a Samu Daga Tarayya: ₦909.9bn
- Gibin da Ke Akwai: Idan har za a bar Kano ta dogara ne kawai a kan kudaden VAT da aka tara a cikin iyakokinta domin gudanar da ayyukanta, ba za su iya biyan ko kashi 10% na ayyukan da ta sa a gaba ba.
Sakamakon tsarin raba kudaden shiga na kasa, Kano tana samun gagarumin kaso daga cikin babban asusun VAT na kasa da ake turo mata, wanda hakan ke nufin tana amfana ne daga irin harajin sayayya da kudancin kasar kamar Lagos da Rivers suka tara.
Amma dogaro da asusun tarayya na bai-daya yana nufin cewa rayuwar ci gaban Kano tana da alaka dumu-dumu da yanayin tattalin arzikin da ke faruwa a kudancin kasar. Wanda wani abu na faruwa a can zai shafi aiyukan da jihar ke gudanarwa.
Kasuwanni suna ci, matsayin jihar a mataki na 7 a kasa yana da kyau, amma babban jarrabawar ita ce yadda za a juya wannan mataki ya haifar da ci gaba.
Ya zama dole ne ga hukumar kididdiga ta jihar Kano ta fara fitar da kididdigar kudaden shigar da ake samu a kasuwanni da sauran wuraren hada-hada son taimakon jihar ta dauki matakan da suka da ce da kuma karfafa kwarin gwuiwar masu zuba jari gami da taimakon masu nazarin tatattalin arziki da sharhi kan cigaban al’umma.





