Mabiya addinin Musulunci da dama na da tantama kan halaccin da yawa daga cikin kasuancin da ake yin shi ta na’ura ko ta Intanet, musamman abin da ya shafi kasuwar hannun jari (Stock Exchange) to idan har kana tantama game da halasci ko haramcin shiga cikin hada-hadar hannayen jari to wannan rubutu zai amfane ka, musamman yanzu da Matatar Dangote ta shiga cikin kasuwar jiya 14/09/2026
Musulman da ke son zuba jari a Matatar Dangote na iya shiga cikin IPO ɗin kamfanin, bayan an tabbatar da cewa tayin hannayen jarin ya dace da ƙa’idojin Shari’ar Musulunci.
Babban aikin Matatar Dangote, wanda ya haɗa da tace ɗanyen mai da samar da man fetur, dizal, man jiragen sama da sinadaran dake da alaka da Fetur, ba ya cikin harkokin kasuwancin da Shari’a ta haramta. A cewar bayanan, kasuwancin makamashi da tace mai halastaccen kasuwanci ne ƙarƙashin dokokin Musulunci.
Bugu da ƙari, kamfanin ya wuce matakan tantance tsarin kuɗinsa da ƙa’idojin AAOIFI, musamman kan bashin da ke ɗauke da ruwa, kuɗaɗen ruwa da sauran kadarorin kuɗi. Binciken ya nuna cewa tsarin kuɗin kamfanin ya kasance cikin iyakokin da ƙa’idojin Shari’a suka amince da su a lokacin IPO.
An kuma ce an gudanar da tantancewar Shari’a tare da bayar da ra’ayi na Shari’a da aka bayyana a cikin takardun IPO, inda ƙungiyoyin ba da shawara kan harkokin kuɗin Musulunci, ciki har da Buraq/Qistal, suka shiga aikin tantancewa.
Sai dai masana harkokin kuɗin Musulunci sun yi gargadin cewa bin Shari’a na iya sauyawa yayin da yanayin kuɗin kamfani ke canzawa. Saboda haka, an shawarci masu hannayen jarin Musulmai da su riƙa bibiyar matsayin kamfanin, sannan idan wani ƙaramin kaso na kuɗin shiga ya fito daga ribar banki, a ware wannan kaso a bayar da shi sadaka domin tsarkake ribar zuba jarin.





