Dakarun rundunar Sojin Najeriya sun ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu ƴan bindiga biyar a wasu hare-hare da suka gudanar a yankin Arewa maso Yamma.
Aiyukan sun kasance wani ɓangare na ci gaba da ƙoƙarin da hukumomin tsaro ke yi na daƙile aiyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun sun kai hare-hare a maboyar ƴan bindiga bayan samun sahihan bayanan sirri, lamarin da ya kai ga kuɓutar da mutanen da aka sace tare da fatattakar maharan. Bugu da ƙari, an kashe ƴan bindiga biyar yayin musayar wuta da jami’an tsaro.
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa waɗanda aka ceto sun samu kulawar da ta dace kafin a fara shirye-shiryen haɗa su da iyalansu. Sun kuma ce ana ci gaba da farautar sauran ƴan bindigar da suka tsere domin tabbatar da tsaron al’umma da hana sake kai hare-hare.
Masu ruwa da tsaki a harkar tsaro sun yaba da nasarar aikin, suna mai cewa irin waɗannan hare-hare na nuna ƙara matsa wa ƙungiyoyin ƴan bindiga lamba a yankunan Arewa maso Yamma. Haka kuma, sun jaddada buƙatar ci gaba da haɗin gwuiwa tsakanin jami’an tsaro da al’umma wajen musayar bayanan sirri.





