Annobar Ƙwalara Ta Hallaka Sama Da Mutane 40 A Borno
Annobar ƙwalara ta yi ajalin sama da mutane 40 tare da kama fiye da mutum 3,000 a sassa daban-daban na Jihar Borno, lamarin da ya jefa hukumomin lafiya cikin fargabar ƙara yaɗuwar cutar. Rahotanni sun nuna cewa annobar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi bakwai da yankuna sama da 130 a jihar. Babban Sakataren Hukumar Kula…


