An Fara Tantance Masu Neman Aikin Ɗamara Na Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta fara tantance waɗanda suka nemi aiki a Hukumar Tsaro ta (NSCDC), Hukumar Shige da Fice (Immigration) da Hukumar Kashe Gobara (Fire Service), a matsayin wani sabon mataki na ɗaukar ma’aikata a hukumomin tsaro na ƙasar. Tantancewar na ƙarƙashin Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB).

Bayan kammala matakin tantance sunayen waɗanda suka nema da kuma gwajin CBT, an buƙaci waɗanda aka zaɓa su shiga shafin hukuma domin duba matsayinsu da bin umarnin mataki na gaba. Haka zalika, tantancewar za ta haɗa da binciken takardu, tantance sahihancin bayanai da kuma duba ƙoshin lafiyar masu neman aikin.

Hukumar ta gargadi masu neman aikin da su dogara kacokan ga bayanan da ake fitarwa a shafin hukuma na CDCFIB, tare da yin hattara da masu damfara da ke ikirarin za su taimaka wajen samun gurbin aiki. Bugu da ƙari, ta jaddada cewa aikin ɗaukar ma’aikatan zai kasance bisa gaskiya da cancanta.

Ana sa ran wannan mataki zai taimaka wajen ƙarfafa hukumomin tsaro ta hanyar ƙara sabbin ma’aikata domin inganta tsaro da ayyukan ceto a faɗin Nijeriya. Masu neman aikin da aka zaɓa an shawarce su da su ci gaba da bibiyar sanarwa daga hukumomin da abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *