Annobar Ƙwalara Ta Hallaka Sama Da Mutane 40 A Borno

Annobar ƙwalara ta yi ajalin sama da mutane 40 tare da kama fiye da mutum 3,000 a sassa daban-daban na Jihar Borno, lamarin da ya jefa hukumomin lafiya cikin fargabar ƙara yaɗuwar cutar. Rahotanni sun nuna cewa annobar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi bakwai da yankuna sama da 130 a jihar.

Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya ta Borno, Dakta Saleh Abba-Kaza, ya ce an fara samun rahotannin waɗanda ake zargi sun kamu da cutar ne a ranar 1 ga Mayu, kafin a tabbatar da ɓarkewar ta a ranar 4 ga watan. Ya bayyana lamarin a matsayin babbar barazana ga lafiyar jama’a, musamman yayin da ake ci gaba da samun sabbin masu ɗauke da cutar.

Rahotannin sun nuna cewa Maiduguri da Jere ne suka fi yawan masu kamuwa da cutar, yayin da aka samu sababbin masu ɗauke da ita sama da 100 cikin sa’o’i 24 a wasu lokuta. Haka zalika, matsalolin tsaftar muhalli da gurɓacewar hanyoyin ruwa na daga cikin abubuwan da ake dangantawa da yaɗuwar annobar.

Gwamnatin Jihar Borno ta ce ta ƙara ɗaukar matakan daƙile cutar ta hanyar samar da magunguna, da kayan tsafta da wayar da kan jama’a. Haka kuma, ta yi kira ga mazauna jihar su kiyaye tsaftar muhalli tare da gaggauta zuwa cibiyoyin lafiya idan suka fara alamomin cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *