A cikin al’ummar Hausawa, mallakar gida ba kawai buri ba ne, alama ce ta cika nauyin da ake ɗora wa namiji, musamman idan ya zo batun samar wa iyali mafaka mai ɗorewa.
Duk da haka, bayan wannan buri mai girma, akwai doguwar tafiya mai cike da ƙalubale, da wahala da sadaukarwa, wadda sau da yawa ba a ganin zurfinta.
Komai yana farawa ne da sayan fili, mataki na farko da ke buƙatar kuɗi mai yawa da kuma juriya wajen neman wuri mai kyau. Bayan haka sai a shiga aikin foundation, wanda shi ne ginshiƙin ginin gaba ɗaya. Idan wannan ya kafu, sai a fara fara gini, daga nan ake ci gaba da zuba ƙasar chiko domin daidaita ƙasa da ƙarfafa tushe.
Bayan haka sai zuba linta, wanda ke tabbatar da cewa bangon gida ya samu ƙarfi. Daga nan kuma sai a ci gaba da ɗora gini, inda tsarin gidan ke fara bayyana. Amma kafin a ji daɗin hakan, sai an kai ga matakan saka ƙofofin ɗakuna da na gaban gida (gare), tare da rafta da buga kwano, domin rufin ya samu cikakken tsari.
Haka kuma, ana buƙatar saka taga (windows) da ƙarafunan kariya (burglars) domin tsaro, sannan a yi aikin lantarki (electric wiring), wanda ke buƙatar ƙwarewa da kuɗi mai yawa. Ba a nan ne wahala ke ƙarewa ba, akwai kuma aikin masai (soak away) da aikin jan ruwa zuwa ko ina a gidan (plumbing), wanda ke da matuƙar muhimmanci ga tsafta da lafiya.
A gefe guda, sai a samar da kayan bandaki, kafin a shiga aikin plaster, wanda ke ba bangon gida laushi sumul. Bayan haka sai a shimfiɗa daɓen zamani (tiles), sannan a yi adon saman ɗakuna (P.O.P), domin ƙawata cikin gida. Daga nan sai a yi filastar zamani (screeding da kuma fenti (painting), wanda ke ba gidan ƙyan gani na ƙarshe.
Amma har yanzu akwai sauran aiki da kamar saka kayan lantarki (electronic fittings), da kuma samar da burtsatsai (borehole da na’urar samar ta wutar lantarki ta Sola (solar), musamman a wannan zamani da wutar lantarki ke wahalar samu. Waɗannan duk matakai ne da namiji ke tsallakewa, sau da yawa cikin damuwa, da cin bashi, da kuma sadaukar da abubuwan jin daɗinsa.
A haƙƙanin gaskiya, gina gida ba aiki ba ne na rana ɗaya. Tafiya ce mai tsawo wadda ke gwada haƙuri, da jajircewa da ƙarfin zuciya.
Yawancin maza na shiga wannan tafiya ne domin su samar wa matansu da ‘ya’yansu mafaka mai aminci, duk da cewa hakan na zo da tsadar gaske ta fuskar kuɗi da kuma lafiyar zuciya.
Saboda haka, ya dace a fahimci irin wannan gwagwarmaya da maza ke yi a ɓoye. Su ne ke ɗaukar nauyin da ba kowa ke gani ba, suna sadaukar da lokacinsu da kuɗinsu domin ganin iyalinsu sun zauna cikin kwanciyar hankali.
Allah Ya taimaki duk wanda ke ƙoƙarin gina gidan kansa, Ya buɗa masa hanyoyin alheri, Ya sauƙaƙa masa wannan tafiya mai cike da ƙalubale.





