Bincike: Shin Jihar Kano Ce Za Ta Fara Aiwatar Da Sabon Albashi Na Naira 70,000?

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi ikirarin cewa jiharsa ce za ta fara aiwatar da sabon albashi na Naira 70,000. Jaridar Leadership ta ruwaito cewa gwamnan ya yi wannan ikirari ne a wani taron bita kan kwadago da aka gudanar a Cibiyar Koyon Aikin Kwadago ta Michael Imoudu da ke Kaduna.

Ikirarin Gwmanan: Gwamnatin Jihar Kano za ta fara aiwatar da sabon albashi na Naira 70,000 a kasar nan.

KARANATA: Daga Ƙarshe Gwamnatin Gombe Ta Amince Da Biyan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

Karin Albashi: Za’a Kara Alawus Na Yan Yiwa Kasa Hidima – NYSC

Karya

Sabanin ikirarin cewa Jihar Kano ce za ta fara aiwatar da sabon albashi na Naira 70,000, binciken da WikkiTimes ta gudanar ya gano cewa jihohin Adamawa da Edo tuni suka fara biyan sabon tsarin albashin ga ma’aikatan su.

Cikakken Bayanin

A ranar Jumma’a, 13 ga watan Satumba na wannan shekara, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa jiharsa zata zama na farko wajen fara aiwatar da sabon albashi na Naira 70,000 a fadin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana hakan a Kaduna yayin wani taron bita na Cibiyar Koyon Aikin Kwadago ta Michael Imoudu kan wanda akayiwa taken “Hanyar Inganta Yanayin Alaka Tsakanin Ma’aikata” da aka shirya wa kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kano NLC da sauran kungiyoyin da ke hade da ita.

Gwamnan, wanda Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano, Abdullahi Musa, ya wakilta, ya tabbatar da cewa jiharsa za ta fara aiwatar da sabon albashi.

“Don tabbatar da wannan, kuma don nuna irin matakin da gwamnatin take dauka game da aiwatar da sabon albashi, mun zo Kaduna don gudanar da wani taron bita musamman kan batutuwan da suka shafi sabon albashi a Jihar Kano”, in ji shi.

DUBA WANNAN: Kano: Majalisa Ta Amince Da Kara N99bn A Kasafin Kudi Domin Fara Biyan Karin Albashi

Gwamna Fintiri Ya Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi

Majalisa Ta Amince Da Dokar N70,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi

A baya, Gwamna Yusuf ya kafa wani kwamiti na ba da shawara kan aiwatar da sabon albashi a watan Agustan 2024.

“Dukkan mambobin kwamitin ba da shawara suna nan a Kaduna don tattaunawa kan batun sabon albashi, don mu iya kammala aikin, kuma da fatan nan da mako mai zuwa za mu gabatar da rahotonmu ga gwamna don daukar mataki. Saboda haka, da yardar Allah, mu ne za mu fara aiwatar da wannan sabon albashi.”

Jaridar Leadership ta wallafa labarin tare da ambaton gwamnan yana yin wannan ikirari.

Tantancewa

Sai dai, binciken gaskiya na Wikkitimes ya nuna cewa jihohin Adamawa da Edo sun riga sun fara biyan ma’aikatan su sabon albashi na Naira 70,000 tun a watan Agusta.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya amince da biyan sabon albashi na Naira 70,000 ga ma’aikatan gwamnatin jiha da na kananan hukumomi.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) a Jihar Adamawa, Kwamared Emmanuel Fashe, ya tabbatar da cewa ma’aikata na matakin jiha sun fara karbar sabon albashin tun a watan Agustan 2024, yayin da ma’aikatan matakin kananan hukumomi za su fara karba a watan Satumba.

Jihar Edo

Gwamnatin Jihar Edo, karkashin Gwamna Godwin Obaseki, ta fara biyan sabon albashi na Naira 70,000 tun a watan Mayun 2024.

Yayin kaddamar da gidan kwadago a birnin Benin, gwamnan ya tabbatar da karin albashi daga Naira 40,000 zuwa Naira 70,000 don rage radadin wahalar tattalin arziki da ma’aikata ke fuskanta.

Duk da cewa Jihar Kano na kokarin aiwatar da sabon tsarin albashi, ba daidai ba ne ma hukuntan jihar suyi ikirarin cewa zasu zamnto na farko wajen fara biyan sabon tsarin albashin, domin jihohin Adamawa da Edo sun riga sun fara biyan ma’aikatan su sabon albashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *