EFCC Ta Ƙwato Biliyan 38.66 Da Wasu Manyan Kadarori

Hukumar EFCC ta samu gagarumar nasara a yaki da cin hanci da rashawa, inda ta kwato tsabar kuɗi har Naira biliyan 38.66 ($38.66bn). Bayan kuɗaɗen, hukumar ta kuma kwace wasu manyan kadarori na miliyoyin nairori yayin da take tsaka da gudanar da bincike mai zurfi kan zambar da ta shafi kwangilolin gyaran matatun man fetur na gwamnatin tarayya.

Wannan bincike na EFCC ya biyo bayan zargin tafka sata, da almubazzaranci, da kuma biyan kuɗaɗen ayyukan da ba a ƙarasa su ba ko waɗanda ma ba a aiwatar da su ba kwata-kwata da sunan farfaɗo da matatun man Najeriya.

Hukumar ta gano cewa an karkatar da manyan kuɗaɗen da aka ware domin gyaran matatun zuwa asusun wasu kamfanonin bogi da kuma ɗaiɗaikun mutane da ke da alaƙa da tsofaffin jami’an gwamnati.

Shugaban hukumar ta EFCC ya jaddada cewa wannan ƙwato kuɗi babban mataki ne da ke nuna cewa gwamnati ba za ta raga wa kowa ba wajen kare dukiyar ƙasa.

Hukumar ta kuma kulle asusun banki da dama na kamfanonin da abin ya shafa, yayin da take shirin gurfanar da dukan mutanen da aka samu da laifi a gaban kotu domin su fuskanci hukunci daidai da doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *