Farashin kayan lambu a kasuwannin Kano ya ragu sosai sakamakon ƙarin yawan kayan amfanin gona da manoma ke kawowa kasuwanni. Wani binciken kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a kasuwannin Yankaba, da kasuwar titin Gwarzo da wasu sassan birnin Kano ya nuna cewa ƙaramin kwandon tumatir yanzu ana sayar da shi kan ₦4,000, daga ₦10,000, wato raguwar kashi 60 cikin 100.
Haka kuma, farashin barkono ya sauka daga ₦9,000 zuwa ₦4,000, yayin da attarugu ya ragu daga ₦10,000 zuwa ₦4,000. Wani ɗan kasuwa, Malam Musa Isyaku, ya ce ana sa ran farashin zai ci gaba da sauka har zuwa ƙarshen damina saboda ƙarin kayan lambun da ake kawowa kasuwanni.
Sai dai Isyaku ya ce rashin isassun wuraren adana kayan lambu na ci gaba da zama babban ƙalubale, musamman ga masu sayar da tumatir, saboda kayan na lalacewa sakamakon zafi da sauyin yanayi.
Ya yi kira ga gwamnati da ta samar da wuraren ajiya, tare da roƙon kamfanoni masu zaman kansu su saka jari a ƙananan wuraren adanawa da sarrafa kayan lambu.





