Illoli 20 Na Zina Masu Haɗari

Akwai zunubai da mutum kan aikata cikin ɗan daɗi, amma ya fuskanci sakamakonsu na tsawon lokaci. Zina na daga cikin manyan zunubai da Musulunci ya yi gargaɗi a kansu, ba wai don kare mutuncin mutum kaɗai ba, har ma don kiyaye iyali, tarbiyya da zaman lafiyar al’umma.

Shin ka san illolin zina guda 20 da ya kamata kowane Musulmi ya sani domin ya nisance ta, ya kuma kiyaye kansa daga hanyoyin da ke kaiwa gare ta?. Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yayi wani rubutu don tunatarwa akai.

Karanta waɗannan illoli, ka yi tunani, kuma ka yaɗa domin tunatar da wasu. Wataƙila wannan tunatarwar ta zama sanadin shiriya ga wani.Allah Ya tsare mu daga zina da dukkan alfasha. Amin.

1. Zina tana jawo fushin Allah Maɗaukaki.

2. Tana rage albarka a rayuwa da arziki.

3. Tana lalata tarbiyyar mutum da mutuncinsa.

4. Tana jawo kunyata a duniya da lahira.

5. Tana raunana imani da tsoron Allah.

6. Tana haifar da yawaitar rabuwar aure.

7. Tana rushe amana tsakanin ma’aurata.

8. Tana haddasa rikice-rikicen iyali.

9. Tana jawo yaɗuwar cututtuka masu haɗari.

10. Tana haifar da ɗaukar ciki ba tare da aure ba.

11. Tana haddasa zubar da ciki da kashe rayuka.

12. Tana jawo rikicin nasaba da rashin sanin uba.

13. Tana lalata tarbiyyar yara da makomar al’umma.

14. Tana jawo damuwa, nadama da tashin hankali.

15. Tana rage ƙima da darajar mutum a idon jama’a.

16. Tana iya kai mutum ga talauci saboda kashe dukiya a haram.

17. Tana buɗe ƙofofin wasu zunubai kamar ƙarya da yaudara.

18. Tana karya zaman lafiya da kwanciyar hankali a al’umma.

19. Tana hana karɓuwar wasu ibadu idan ba a tuba ba.

20. Tana jawo azaba mai tsanani idan mutum bai tuba ba.Allah Ya ce: ﴾“Kada ku kusanci zina; lallai ita alfasha ce kuma mummunar hanya ce.”— Al-Qur’ani Mai GirmaAllah Ya tsare mu daga zina da duk hanyoyin da ke kaiwa gare ta, Ya kuma azurta mu da tsarki da kamun kai. Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *