Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ta fitar da cikakken jadawalin yadda ƙasashen da suka rage za su fafata a zagaye na 32 na gasar Kofin Duniya. Wannan zagaye na zuwa ne da wasanni masu zafi da za su gamsar da masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya, inda manyan ƙasashen duniya za su kece raini domin neman gurbi a zagaye na gaba.
A cikin manyan wasannin da ake dako, akwai fafatawa tsakanin ƙasar Jamus (Germany) da Paraguay, yayin da ƙasar Faransa (France) za ta kece raini da Sweden. Manyan ƙasashen Turai irin su Netherlands za su gwada kwazonsu da Morocco, yayin da Portugal za ta kara da takwararta ta Croatia a wani wasa mai zafi da ake sa ran zai ɗauki hankali ƙwarai da aniya.
Haka zalika, wakilan nahiyar Afirka zasu sami zarafin fafatawa da ƙasashe daban-daban na duniya. Ƙasar Afirka ta Kudu (South Africa) za ta gwada ƙwazonta da Canada, yayin da Senegal za ta fuskanci Belgium. Ƙasar Ivory Coast kuma za ta haɗu da Norway, yayin da Congo za ta kara da England, ita kuwa Algeria za ta fafata da Switzerland, sai Ghana kuma za ta kara da Colombia.
A sauran wasannin kuma, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brazil za ta kece raini da Japan, yayin da Argentina mai riƙe da kambun za ta fuskanci Cape Verde. Ƙasar Mexico za ta kara da Ecuador, sannan Amurka (USA) za ta kara da Bosnia, ita kuwa Spain za ta fuskanci Austria, yayin da Australia za ta raba reni da ƙasar Egypt.





