Kanu Nwankwo, wanda aka fi sani da “Papilo,” shi ne ɗan ƙwallon ƙafar Nigeria da ya fi kowa samun kofuna da lambobin yabo a tarihi. Tarihinsa a harkar ƙwallon ƙafa na cike da manyan nasarori tun daga gida Nigeria har zuwa matakin duniya.
Kofunan Ƙasashen Turai
Nasarorin Kanu a nahiyar Turai sun kafa sabon babi a tarihin ‘yan wasan Afirka: UEFA Champions League (1): Ya daga kofin Zakarun Turai tare da ƙungiyar Ajax. UEFA Cup (1): Ya lashe kofin tare da ƙungiyar Inter Milan ta ƙasar Italiya. Dutch Eredivisie (3): Ya kafa tarihi ta hanyar lashe gasar Holland sau uku riga-riga.
Nasarar Gasar Firimiyya ta Ingila
A ƙasar Ingila, Kanu ya bar gurbin da ke da wuyar gogewa a tsakanin manyan kulob: English Premier League (2): Ya lashe kofin Premier tare da Arsenal. FA Cup (3): Ya daga kofin ƙalubale na FA Cup sau uku (tare da Arsenal da kuma Portsmouth).
Gasar Ƙasa da Ƙasa da ta Gida
A matakin kasa da kuma gida Nigeria, Papilo ya kafa shafin zinare da ba za a taba mantawa da shi ba: Olympic Gold Medal (1): Ya jagoranci tawagar Nigeria wajen samun lambar zinare a Atlanta 1996. U17 World Cup (1): Ya lashe kofin duniya na matasa a 1993. Nigerian Premier League (1): Ya lashe gasar gida ta Nigeria a farkon sana’arsa.
Lambobin Yabo na Mutum Kansa
Gwanintarsa da basirarsa a fili sun ba shi damar karɓar manyan lambobin yabo na duniya: African Footballer of the Year (2): Ya zama dan wasan Afrika mafi kyau na shekara sau biyu (1996 da 1999). BBC African Footballer of the Year (2): Ya lashe kyautar gwanin Afrika ta BBC sau biyu. Ballon d’Or Ranking: Ya samu matsayi na 6 a jerin ‘yan wasa mafiya kyau a duniya a shekarar 1996.





