Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta samu tsohon Ministan Wuta, Saleh Mamman, da laifi kan zargin sama da faɗi da kuɗi da ake yi masa.
Alƙalin kotun, James Omotosho, ya yanke hukuncin cewa EFCC ta tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon ministan ba tare da wata shakka ba.
Kotun ta same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhume 12 da hukumar EFCC ta shigar a kansa kan badaƙalar kuɗi ta Naira biliyan 33.8.
Saleh Mamman ya kasance Ministan Wuta lantarki a gwamnatin Muhammadu Buhari daga watan Agustan 2019 zuwa Satumban 2021 kafin a cire shi daga muƙaminsa.





