NDLEA Ta Kama Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi 6A Kusa Da BUK A Kano

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen Kano ta kama mutane shida da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi yayin wani sumame a kusa da tsohuwar harabar Jami’ar Bayero Kano (BUK). Haka kuma, hukumar ta rushe wasu wuraren da ake zargin ana sayarwa da shan miyagun ƙwayoyi a yankin.

A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Sadiq Maigatari, ya fitar a ranar Litinin, an gudanar da samamen ne ƙarƙashin jagorancin kwamandan rundunar Kano, CN DY Lawal, bayan ƙorafe-ƙorafe daga mahukuntan jami’ar kan yawaitar ayyukan miyagun ƙwayoyi a yankin.

Bugu da ƙari, Maigatari ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne ƙarƙashin “Operation Sharar Mafaka” domin kawar da maboyar masu laifi da tabbatar da tsaro ga ɗalibai da mazauna yankin. Ya ƙara da cewa an kama waɗanda ake zargin tare da ƙwace kayayyakin da ke da alaƙa da laifukan, inda aka lalata su.

A ƙarshe, hukumar NDLEA ta jaddada aniyarta na tabbatar da muhalli mara miyagun ƙwayoyi a cibiyoyin ilimi, tare da yabawa mahukuntan BUK bisa haɗin kai. Saboda haka, ta gargadi masu aikata irin waɗannan laifuka tare da kira ga jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanai domin gano da rushe irin waɗannan maboyar a faɗin Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *