“Sakamakon binciken mu ya gano cewa da gaske ne ofishin babban mai taimakawa shugaban kasa (SSAP) ya karkatar da buhun shinkafa 500, wanda kudin su ya kama miliyan N31, kuma an tura kudin zuwa asusun banki mai nasaba da shi, duk da har yanzu ofishin mataimakin ya ki amincewa da wannan zargin.”
Wadannan kalamai na sama sun fito ne daga bakin Kwamred Musa Mu’azu Musa, jagoran wata kungiya ta ma su bukata ta musamman (Disability Hub Africa), wanda shine ya kasance a kan gaba wajen bankado yadda aka karkatar da buhun shinkafa 500 da aka damka a hannun ofishin SSAP, Alhaji Mohammed Abba Isa, babban mai taimakawa shugaban kasa a kan harkokin da su ka shafi ma su ta bukata (PWD) a fadin Nigeria.
Kwamred Musa ya yi zargin cewa tun cikin watan Mayu ofishin SSAP Mohammed ya karbi buhun shinkafa 1000 daga ofishin hukumar kwastam a jihar Lagos, domin rabawa ma su bukata ta musamman, amma har zuwa cikin watan Oktoba babu wani bayani a kan yadda aka yi da shinkafar.
Kwamred Musa ya kara da cewa ya samu korafe-korafe har guda bakwai daga kungiyoyi daban-daban na ma su bukata ta musamman da ya ke jagoranta, inda su ka bayyana cewa ba a basu irin wannan shinkafar da hukumar kwastam ta saki domin a raba mu su don su samu saukin matsin tattalin arziki da ake ciki ba.
A cewar Kwamred Musa, daga cikin kungiyoyin da su ka yi korafi akwai kungiyar ma su bukata na musammam daga kudancin Nigeria, kungiyar ma su bukata ta musamman reshen birnin tarayya da takwararta ta ‘yan kabilar Igbo.
Kwamred Musa ya bayyana cewa shi da sauran shugabannin kungiyoyin ma su bukata ta musamman ba su bata lokaci ba wajen fara bincike ta hanyar rubuta takarda zuwa ofishin hukumar kwastam wacce ta basu tabbacin cewa sun bawa SSAP Mohammed shinkafar da ake magana.
Ya kara da cewa hukumar kwastam, bayan tabbatar da sakin buhunhunan shinkafar, sun tabbatar da cewa sun dauki alkawarin bayar da karin wasu kayayyakin da su ka hada da sutura da sauran su ga ma su bukata ta musamman domin inganta rayuwar su.
Kwamred Musa ya cigaba da cewa binciken da su ka fara gudanarwa ya gano cewa an siyar da buhu 500 daga cikin buhu 1000 tare da saka kudin da aka siyar da su a wani asusun bankin Zenith mai alaka da ofishin SSAP Mohammed. Sauran buhu 500 kuma sai aka sake kasafta su zuwa kananan buhunhuna ma su nauyin 10kg, kwatankwacin kwano uku na shinkafa, kafin rabawa wasu tsirarun ma su bukata ta musamman.
A yayin da batun wannan zargi ya dauki zafi, an tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastam, Abdullahi Aliyu, domin ya yi karin haske, wanda ya bayyana cewa bashi da masaniya a kan batun bayar da buhunhunan shinkafar.
Abdullahi ya bayyana cewa hukumar kwastam ba za ta yi irin wannan aiki na bayar da shinkafa ba tare da gayyato kafafen yada labarai ba.
Kazalika, ya kara da cewa hukumar kwastam ta dakatar da rabon shinkafa da sauran kayan masarufi ga mabukata daga cikin al’umma bayan an samu wata turereniya mai muni yayin wani lokacin rabo.
“Ba ma rabon shinkafa. Ba ni da masaniyar cewa hukumar kwastam ta bayar da shinkafa zuwa ofishin shugaban kasa, babu wannan bayanin a wuri na,” a cewar Abdullahi yayin da ya ke amsa tambaya a kan batun bayar da shinkafa ga SSAP domin rabawa ma su bukata ta musamman.
A kokarin gano gaskiyar wannan zargi, an tuntubi SSAP Mohammed ta hanyar kiran sa ta waya amma bai amsa ko daya daga cikin kira ma su yawa da aka yi ma sa a kan lambar sa ta MTN ba, kazalika bai dawo da amsar sakon da aka aika ma sa ba.
Daga baya, misalin karfe 9:00 na daren ranar, ya dawo da kira ta lambar da aka kira shi tare da yin ruwan zage-zage da barazanar lalata rayuwar Dan Jaridar da ya kira shi idan ya sake ya wallafa ”zargi maras tushe” da ake yi ma sa, kamar yadda ya bayyana.
“Kai dan iska ne! kana son ka bata sunan mutumin da ke aiki a ofishin shugaban kasa? ka kira ni ka fada min maganar banza? zan yi maganin ka! zan daure ka,” wadannan sune martanin SSAP Mohammed ga tambayar da aka yi ma sa a kan zargin da ake yi ma sa.
Har ila yau, daga baya ya aika sako zuwa ga Dan Jaridar cikin harshen Hausa kamar haka, “ka ci durun uwarka”.

A kokarin yi wa SSAP Mohammed a kan batun zargin, an tuntubi shugaban ma’aikata na ofishin sa, Barisa Yusuf Iyodo, wanda ya tabbatar da cewa ofishin SSAP Mohammed ya karbi buhun shinkafa 1000 kuma tuni an fara rabawa.
Sai dai, ya musanta zargin cewa an siyar da buhu 500 daga cikin shinkafar ga wani dan kasuwa tare da bayyana cewa akwai buhu 87 daga cikin shinkafar da ruwa ya lalata su. Amma da aka tambaye shi ko zai iya gabatar da wata shaida a kan faruwar hakan sai ya ce:
“Ka hakura da wannan bayanin don bashi da amfani a wurin ka. Wannan bayani ne da bai shafeka ba, kawai na fada maka ne cikin hira.
Tun a baya dai, Kwamred Musa ya yi zargin cewa daga cikin buhu 1000 na shinkafar, an bawa wani babban jami’i a ofishin SSAP Mohammed buhu 60 a matsayin kason sa, zargin da Barista Yusuf ya musanta.
“Mun gano cewa an bawa wani babban jami’i a ofishin SSAP buhu 60 daga cikin shinkafar. Har yanzu mu na bincike dangane da hakan. Wasu daga cikin ma’aikatan ofishin SSAP Mohammed sun yi kokarin bayar da uzuri a kan siyar da wani bangare na shinkafar wanda har yanzu ba a san a kan nawa aka siyar da kowanne buhu ba, mene ne dalilin siyar da shinkafar? sannan, babban abin tambayar shine me ya sa sauran yankunan kasar nan ba a basu ba? a cewar kwamred Musa.
Kwamred Musa ya bayyana cewa Barista Yusuf, yayin musayar yawu tsakaninsu, ya fadi cewa an siyar da wani bangare na shinkafar ne domin daukar dawainiyar dako da tsaron motocin da su ka dauko shinkafar daga Lagos zuwa Abuja.
Sai dai, Kwamred Musa ya ce, “wasu daga cikin amsoshin da mu ka samu daga ofishin SSAP abin dariya ne da kuma takaici wai an siyar don samun kudin biyan dako da jami’an tsaro da su ka raka shinkafar daga Lagos zuwa Abuja.
“Abin da zai baka mamaki shine, tunda daga Lagos aka dauko shinkafar, me ya sa ba za a ware kason mutanen yankin kudu maso yamma ba a can? me ya sa daga can ba za a ware kason mutanen kudu maso kudu ba da na yankin kudu maso gabas ba?, a cewar Kwamred Musa.
Kwamred Musa ya nuna takaicinsa a kan yadda SSAP Mohammed, wanda shi kan sa mai bukata ta musamman ne, da ya kamata ya tausayawa ‘yan uwansa ma su bukata ta musamman amma kuma ya ke cutar da su.
Kamar yadda kwamred Musa da sauran korafi su ka bayyana sun ce za su rubuta takardar korafi zuwa hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki tare da bayyana cewar basa tsoron su tsaya a gabn kotu da SSAP Mohammed domin kare zargin da su ke yi masa.
Kwamred Musa, wanda ya bayyana cewa a wani yanki jihar Nasarawa da Abuja kadai aka raba kananan buhunhuna shinkafa ga ma su bukata ta musamman, ya kara da cewa akwai kwarararn tambayoyi da ya ke so SSAP Mohammed ya amsa domin wanke kan sa daga wannan zargi.
Ya bayyana cewa tambayoyi su ne kamar haka; (1) shin daga ina kudi miliyan N31 ya fito da aka saka a asusun bankin sa na Zenith, shin kudin ba daga siyar da buhu 500 na shinkafa su ka fito ba? (2) shin an bawa wani jami’i a ofishinsa buhu 60 daga cikin shinkafar da aka bayar buhu 1000 ko ba a yi hakan ba? (3) ko an yi adalci wajen rabon shinkafar a tsakanin sassan kasar nan ko ba a yi ba?





